Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, April 13, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaGanduje ya mayar da inda ya rushe a kasuwar Beruit wurin ajiye...

Ganduje ya mayar da inda ya rushe a kasuwar Beruit wurin ajiye ababen hawa

Date:

Ashiru Umar

 

Gwaman Kano Abdullahi Umar Ganduje ya mayar da wurin da bene mai hawa uku ya rikito a kasuwar waya ta Beruit wuri ajiye ababen hawa.

 

Wannan na zuwa ne jim Kadan bayan da gwamnan ya ziyarci kasuwar domin jajantawa wadanda al’amarin ya shafa ranar Laraba.

 

Ganduje ya ce tuni gwamnati ta kafa kwamiti na musamman da zai binciki matsalar domin daukar matakin da ya da ce.

 

Gwamnan ya kuma bukaci al’ummar kasuwar da su baiwa gwamnati hadin kai yayin gudanar da binciken.

 

Ganduje ya bayyana cewa daga yanzu gwamnati ta mayar da inda abin ya faru wurin ajiye ababan hawa.

 

A na sa jawabin shugaban masu saida wayoyi na kasa Alhaji Musa Haruna ya ce ´yan kasuwar sun girgiza bayan da suka tsinkayi zaftarowar ginin babu tsamani.

 

Ya ce amma sun godewa Allah da ba a samu asarar rayuka da yawa ba.

 

Musa Hashim ya kuma godewa gwamnatin Kano dangane da matakin da ta dauka.

 

A jiya ne dai wani bene da ake ginawa mai hawa uku ya rikito a kasuwar inda ya hallaka mutum guda tare da jikkata wasu da dama.

 

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories