Saurari premier Radio
39.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAmbaliyar ruwa ta hallaka mutun 15 a Borno

Ambaliyar ruwa ta hallaka mutun 15 a Borno

Date:

Mukhtar Yahya Usman

A kalla mutane 15 ne suka mutu a  kogin Ngadabulu da ke Maidugurin jihar Borno sakamakon ambaliyar ruwa

Jami’in hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA a arewa maso gabas Muhammad Usman, ne ya bayyana hakan a jiya Laraba, a Maiduguri.

Usman ya ce ana samun karuwar mutane da ke nutsewa cikin kogin sakamakon ambaliya wanda kuma ya shafi al’ummomi da ke kusa da bakin kogin a Maiduguri.

Ya bukaci iyaye da su gargadi ‘ya’yansu kan yin ninkaya a kogin domin kaucewa nutsewa.

Jami’in na NEMA ya kara da cewa hukumar ta samar da kayakin agaji da za ta baiwa wadanda ambaliyar ta shafa inda kuma take wayar da kan al’umma kan haduran ambaliyar ruwa da kuma hanyoyi da za su kare kansu.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories