Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Thursday, April 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiEFCC ta cafke shugaban majalisar dokokin jihar Ogun

EFCC ta cafke shugaban majalisar dokokin jihar Ogun

Date:

Hafsat Bello Bahara

Hukumar  EFCC, ta cafke shugaban majalisar dokokin jihar Ogun, Hon. Olakunle Oluomo.

Rahotanni  sun ce an kama Oluomo ne da misalin karfe 9 na safiyar yau Alhamis a filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Legas.

rahotanin sun kara da cewa jami’an hukumar EFCC ne suka cafke shi domin ya amsa tambayoyin da suka shafi almundahanar wasu kudade.

Kawo yanzu  Hukumar ta EFCC ba ta tabbatar da kama dan majalisar ba  amma ana sa ran nan ba da jimawa ba za su fitar da sanarwa.

Sai dai wata majiya a cikin Hukumar ta EFCC ta tabbatar da cewa hukumar ta gayyaci Shugaban majalisar lokuta da dama amma ya kasa amsa gayyatar.

Yanzu haka dai an kai shi ofishin EFCC na birnin Legas don ci gaba da yi masa tambayoyi.

Latest stories

Hukumar EFCC ta musalta zargin da ake mata na fara bincikar tsohon Gwamnan kogi.

Shugaban hukumar EFCC mai hukunta masu yiwa tattalin arziki...

Majalisar dokokin Kano ta nemi a dakatar da KEDCO kan yanke wuta.

Majalisar Dokokin jihar Kano ta bukaci gwamnatin jihar data...

Related stories