Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWata gwarzuwar daliba ta rabauta da tallafin karatu a jami'ar kawu Sumaila

Wata gwarzuwar daliba ta rabauta da tallafin karatu a jami’ar kawu Sumaila

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Mamallakin Jami’ar Al-Istiqama Suma’il, Alhaji Abdurrahman Kawu Sumaila ya biwai wata daliba mai kwazo Rumasa’u Muhammad Adam gurbin karatu a jami’ar tasa.

 

wannan ya biyo bayan kwazon da dalibar ta nuna inda ta samu sakamako mai kyau a jarrabawar kammala sakandire ta WAEC.

 

Dalibar dai yar asalin garin Kachako ce ta samu nasarar cinye dukkanin darinsa da ta rubuta jarrabawa akansu guda tara.

 

da yake jawabin jim kadan bayan baiwa dalibar tallafin Hon Kawu Sumaila ya ce yadda yake alfahari da ilimi a cikin al’umma ne ya sanyashi tallafa mata.

 An ba ta izinin yin karatun digiri na shekaru hudu a tsangayar koyar da ilimin kimiyya lafiya a Jami’ar AL-Istiqama, Sumaila, farawa daga shekarar karatu ta 2022/2023 .
 A lokacin da yake mika godiyarsa ga Kawu Sumaila bisa karamcin da ya yiwa yar, Hon. Hamza Safiyanu Kachako, a madadin al’ummar Takai/Kachako, ya mika godiyarsa ga Allah madaukakin sarki, ya kuma yabawa Kawu Sumaila bisa wannan karimcin.

Latest stories

Related stories