30.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaraiKarota ta kama mota makare da giya

Karota ta kama mota makare da giya

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

 

A karo na biyu ƙasa da mako guda, hukumar kula da Zirga-zirga Ababen hawa ta jiha Kano (KAROTA) ta ƙara kama mota ƙirar Tirela maƙare da Giya.

 

Ba jami’in mu ne ke shan giya a wani faifan bidiyo ba- KAROTA

 

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin hukumar Nabulisi Abubakar Kofar Na’isa, ya fitar a Alhamis din nan.

 

Hukumar ta sami nasarar kama Tirelar ne a kan titin Bello Dandago da misalin karfe 2:30 na daren Larabar da ta gabata, a ƙoƙarin su na shiga cikin Sabon Garin Kano.

 

Jami’an Hukumar ne suka kama motar a lokacin da suka buƙaci direban motar ya gabatar musu da takardar shaidar abinda ya ɗakko ta Way bill, inda ya bayyana musu cewa Kwali ya ɗakko.

 

Bayan da jami’an suka matsa bincike sai suka tabbatar da Giya ce a cikin babbar motar.

 

Shugaban Hukumar KAROTA Hon Baffa Babba Ɗan’agundi ya bayyana cewa Hukumar KAROTA ba za ta gajiya ba wajen kama duk wani nau’in kayan da aka ci garo da su wanda dokar jihar Kano bata amince a shigo da su ba.

 

Ya ƙara da cewa za a ƙara baza jami’an KAROTA musamman kan manyan titinan jihar nan domin ganin an daƙile shigowar kayayyakin da dokar jihar Kano ta haramta.

 

Ƙasa da sati guda hukumar ta cafke manyan motocin Tirela maƙare da Giya wadanda adadinta ya kai fiye da Kwalba dubu arba’in (K40)da kuɗinta ya haura naira miliyan arba’in (N40m).

 

Da zarar an kammala bincike za a miƙa Giyar ga Hukumar Hizba domin ɗaukar mataki na gaba.
.

Latest stories