Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Saturday, April 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasu Mabaratan Yan Leken Asiri Ne - Hisbah

Wasu Mabaratan Yan Leken Asiri Ne – Hisbah

Date:

Babban Kwamandan Hukumar Hisbah Muhammad Haruna Ibn Sina yace hukumar ta lura da yadda ake amfani da wasu mabarata a matsayin ’yan leken asiri da debowa wasu bata gari labarai, wanda hakan ke kawo barazana ga tsaro a jihar.

 

A cigaba da yunkurin da Hukumar Hisbah ta Jihar Kano take yi na tsaftace jihar ta ce ta fara dakile barace-barace a kan titunan jihar.

 

Ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai game da ayyukansu inda yace hukumar na cigaba da yunkurin tsaftace jihar ta hanyar fara dakile barace-barace a kan tituna a jihar.

 

Ibn Sina ya kuma kara da cewa a cikin makonni biyu hukumar ta kama wasu mabarata 931 da suka hadar da maza da mata wanda wasu daga cikin su ba yan jihar Kano ba.

 

Daga bisani ya kuma ce mabaratan da aka kama fiye da sau daya za a gurfanar da su gaban kuliya, yayin da yara mabarata, wadanda ba a iya tantance iyayansu ba za a shigar da su makarantu.

Latest stories

Related stories