Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiRikicin PDP: Tsagin Wike,Sun Gabatar da Taron Sirri a Birnin Landan

Rikicin PDP: Tsagin Wike,Sun Gabatar da Taron Sirri a Birnin Landan

Date:

Rikicin Tsagin Wike da Atiku Abubakar na cigaba da kamari biyo bayan gaza samun hadin kai tsakanin bangarorin da ke rikici da juna a jam’iyyar ta PDP. Gwamnan Ribas, Nyesom Wike da wasu abokansa sun sake komawa birnin Landan don wani taron Sirrin.

 

Idan za’a iya tunawa Atiku ya gana da Wike da wasu abokansa a Landan makonni biyu da suka gabata. Rahotanni sun bayyana cewa dan takarar shugaban kasar ya tattauna da gwamnonin kan bukatar jam’iyyar PDP ta haɗa kan ƴaƴan ta gabannin babban zaben 2023.

 

Sai dai bayan wannan tattaunawa Wike da Sanata Iyioricha Ayu, shugaban jam’iyyar na kasa, sun sake sabunta kiyayya ta hanyar musayar kalamai a kafafen yada labarai a Yan kwanakin nan.

 

Bayan wannan zazzafar cecekuce, Wike da magoya bayansa ciki har da gwamnan jihar Benue Samuel Ortom, sun nufi birnin Landan.

 

Inda ake kyautata zaton taron na Landan an yi shi ne don samar da dabarun tabbatar da nasara gabanni taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) da na kwamitin ayyuka na kasa (NWC) da jam’iyyar da za gabatar kafin a kafa kwamitin yakin neman zaben PDP a cikin makon da muke ciki.

 

Ana sa ran wannan taron yana da nasaba da tsaida magana daya ko bangaren Wike zasu karbi wani matsayin a cikin kwamitin yakin neman zaben.

 

Wata majiya ta shaidawa jaridar Daily Trust cewa bayan ganawar da suka yi da dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar a birnin Landan a wancen karan

 

“Bangaren Wike sun yi fatan Atiku zai yi nasara akan shugaban jam’iyyar na kasa Ayu ya bar mukaminsa. Amma abin da ya faru na ‘yan kwanakin nan na iya canza yanayin rikicin gaba ɗaya. Kamar dai bangarorin biyu ba su da niyyar janye kudurin su. Na yi imanin suna so su sake tsara dabarun su kuma su yanke shawarar irin matakin da za su taka a kwamitin yakin neman zaben,” inji majiyar.

 

A makon da ya gabata, Wike ya yi alkawarin cewa “wani abu zai faru nan ba da jimawa ba” a cikin PDP, kodayake bai ambaci ainihin abin da ze farun ba.

 

Gwamnan Ribas ya kuma ce zai taimaka wa Shugaban jam’iyyar na kasa don ganin PDP ta fadi zabe a 2023 tunda a cewarsa Ayu da kansa ba ya son jam’iyyar ta ci zabe.

 

Hakan ya biyo bayan zargin shugaban jam’iyyar da kin sauka daga mulki saboda naira biliyan 14 da ke cikin asusun jam’iyyar.

 

A wannan makon ne ake sa ran manyan jigajigan jam’iyyar za su yi taro domin amincewa da kafa kwamitin yakin neman zaben.

 

Za kuma su duba rikicin da ke faruwa a jam’iyyar domin ganin ko har yanzu za su iya ceto lamarin kafin lokaci ya kure musu.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories