Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYanzu-yanzu: Wani gini mai hawa 7 ya ruguzo a Legas

Yanzu-yanzu: Wani gini mai hawa 7 ya ruguzo a Legas

Date:

Wani gini mai hawa bakwai da ba a kammala ba ya rushe a birnin Legas na inda ya ritsa da mutane da dama.

Rahotanni na cewa ginin, wanda ke kan Titin Oba Idowu Oniru, ya ritsa da mutum kusan shida bayan faɗowarsa a cikin dare wayewar garin Lahadi.

Sakataren hukumar agajin gaggawa reshen Jihar Legas, Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce tuni suka ƙaddamar da aikin ceton waɗanda ginin ya rufe.

“Zuwanmu wurin ke da wuya muka tarar ginin mai hawa bakwai da ba a kammala ba ya rikito,” a cewarsa.

“Babu rahoton ko wani ya ji rauni amma ana zaton ɓaraguzai sun rufe mutum shida.”

Ya ƙara da cewa ma’aikatansu na buƙatar “manyan kayan aiki” a yunƙurin ceto mutanen.

Ya ce sun ƙaddamar da “shirin aikin ceto na gaggawa na Jihar Legas”.

A makon da ya gabata ma wani gini mai hawa uku ya faɗo a kasuwar sayar da wayoyi ta Beirut a nan  Kano, wanda ya jawo asarar rayuka.

Latest stories

Related stories