33.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabaran KanoZa'a Kara Harajin Makarantun Gaba da Sakandire

Za’a Kara Harajin Makarantun Gaba da Sakandire

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

ABDULRASHID HUSSAIN

Kwamitin Ilimi na Majalisar Dattawa ya ce akwai bukatar karin harajin makarantun gaba da sakandare daga kashi 2.5 zuwa kashi uku, domin inganta ayyukan gwaje-gwaje da bincike a kasar nan.

 

Kwamitin ya bayyana hakan ne yayin ziyararsa ga shugabannin asusun tallafawa manyan makarantu domin duba ayyukan kasafin hukumar na 2021 zuwa 2022.

 

Kwamitin, karkashin jagorancin Sanata Ahmad Babba Kaita, ya bukaci asusun ya sanya cibiyar lissafi ta kasa a jerin wadanda za su dinga bai wa tallafin, domin babu wata kasa da za ta ci gaba a fannin bincike da kimiyya da fasaha da kuma kirkire-kirkire, ba tare da ta rungumi ilmin lissafi ba.

 

Ya kuma ce akwai bukatar hukumar ta kara dagewa wajen samar da na’urar bada iskar Oxygen da a baya kwalejin fasaha ta kaduna ta bukata, lokacin da duniya ta yi fama da cutar COVID-19.

 

A nasa bangaren babbabn sakataren asusun Sonny Echono, ya ce, tuni hukumar ta amince da fitar da Naira miliyan 50 domin fara samar da iskar, har ma ta biya rabin kudin.

 

Ya kuma ce a bara kadai, hukumar ta rabawa makarantun gaba da sakandare tallafin sama da Naira miliyan dubu dari 2 ciki har da sabbi da suka fara aiki a shekarar.

Latest stories