24.9 C
Kano
Sunday, June 4, 2023
HomeLabarai'Yan sanda a Kebbi sun kama matar da ta kashe mijinta

‘Yan sanda a Kebbi sun kama matar da ta kashe mijinta

Date:

Related stories

Maniyyata 17,000 ne suka bar Najeriya zuwa kasa maitsarki-NAHCON

Bayan kwashe kwanaki bakwai da fara jigilar alhazan Najeriya...

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kebbi ta kama wata mata da ake zargi da kashe tsohon mijinta.

Tsohon mijin mata alƙalin kotun majistare ne mai suna Attahiru Ibrahim Zagga.

Kakakin rundunar, SP Nafiu Abubakar, ya shaidawq manema labarai cewa da misalin ƙarfe 9:00 na dare ranar Alhamis ne maƙota suka kai musu rahoton cewa sun ji hayaniya a gidan alƙalin da ke unguwar Alieru a birnin Kebbi.

Da isar jami’ansu ne kuma suka tarar da Attahiru kwance cikin jini, inda suka garzaya da shi asibita kuma a can ne likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

“Bayan shigar jami’anmu gidan suka tarar da tsohuwar matarsa mai suna Farida Abubakar kuma aka kama ta da zargin hannunta a aikata kisan,” in ji SP Nafiu.

Kafin mutuwarsa, Attahiru Ibrahim alƙalin kotun majistare ne a garin Jega na Ƙaramar Hukumar Jega.

Latest stories