Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKasuwanciMa'aunin tattalin arzikin kasa GDP ya karu da kaso 3.54 -NBS

Ma’aunin tattalin arzikin kasa GDP ya karu da kaso 3.54 -NBS

Date:

Hafsat Bello Bahara

Hukumar kididdiga ta kasa NBS ta ce ma’aunin tattalin arzikin kasa ya karu da kaso 3.54 a watanni shidan farkon wanna shekara.

Wannan na kunshe cikin wani jawabi da shugaban hukumar Prince Seminu Adeniran ya fitar a ranar juma’a a birnin tarayya Abuja.

Mista Adeniran ya ce a watannin shidan farko na wannan shekarar ma’ aunin arzikin kasa ya kai kimanin naira triliyan 45 da biliyan 32 wanda ya karu da kaso 15 cikin dari akan adadin Idan aka kwatanta da bara.

Mista Adeniran ya kara da cewar a wannan karon an samu raguwar cinikin danyan manfetur saboda karuwar fashinsa da bata gari ke yi ta hanyar fasa bututun mai.

“A shekarar da ta gabata akan samar da ganga miliyan 1 da dubu 61 a kowace rana a wannan karon ansamu ganga miliyan daya da dubu 43 a kowace rana.”

Mista Adeniran ya kuma bayyana cewar kafafan sadarwa, cinikayya, sufuri, noma da kirkira ne suka taimaka wajen samun karuwar adadin ma’aunin tattalin arzikin a wannan karon.

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...