Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKungiyar lauyoyi NBA za ta hukunta barayin mambobinta

Kungiyar lauyoyi NBA za ta hukunta barayin mambobinta

Date:

Hafsat Bello Bahara

Kungiyar lauyoyi ta kasa NBA ta ce za ta hukunta lauyoyin da suka saci wayoyi a taron Kungiyar na ranar Talata.

 

Shugaban kungiyar Olamide Akpata ne ya bayyana hakan  yayin da yake tsokaci kan wani faifan Bediyo da ke yawo akafafen sada zumuta.

 

Faifan bidoyon dai ya nuna wasu lauyoyin na wawason kayayyakin da aka tanada domin rabawa lokacin Taron kungiyar a jihar Lagos.

 

Mista Akpata ya ce wasu lauyoyin sun fake da bacin ran rashin samun kayan da aka raba yasa su fasa inda aka ajiye kayayakin suka kuma sace.

 

Cikin abinda suka sata har da wayoyi sa jakunkuna tare da yiwa wasu maikatan otal din da aka yi taron dukan tsiya.

 

Ya ce wannan abu ya taba martaba da darajar kungiyar, a don haka ya zama sole su hukunta masu laifin.

 

A cewarsa da zarar sun kammala bincike za su hukunta dukkan wanda aka tabbatar na da hannun wajen aikata wannan danyen aikin.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories