Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAkwai yuwuwar Najeriya ta cike gibin kasafin 2023 da bashin naira tiriliyan...

Akwai yuwuwar Najeriya ta cike gibin kasafin 2023 da bashin naira tiriliyan 11

Date:

Muhammad Bello Dabai

 

Bayanai na nuna cewar Najeriya na gab da matsawa mataki na gaba a jadawalin kasashe mafiya cin bashin bankin duniya, wanda a baya ya bayyana ta a mataki na 4.

 

Tabbatuwar hakan, ka iya biyo bayan amincewa kudirin gwamnatin tarayya wajen ciyo bashin naira triliyan 11 da biliyan 3, domin cike gibin kasafin kudin badi.

 

A ranar litinin ne ministar kudi kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmad Shamsuna ta gabatarwa majalisar wakilai ta kasa kudirin kasafin na shekarar 2023, wanda adadinsa ya doshi naira triliyan 20.

 

Ministar kudin tace gwamnatin tarayya na sa ran samun kudin shiga na naira triliyan 8 da biliyan 46 a shekara mai zuwa, inda bangaren arzikin mai na kasa ake sa ran zai samar da triliyan 2.

 

Zainab Ahmad Shamsuna tace an dora kiyasin kudin ne bisa farashin gangar mai kan dala 70 da kuma darajar naira akan 436 duk dala daya.

 

Har ila yau an yi kiyasin fitar da gangar mai miliyan 1 da dubu 690 a kullum.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...