Saurari premier Radio
37.5 C
Kano
Tuesday, June 25, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin KanoAmbaliya:Gwamnatin Kano za ta rushe gine-ginen da akayi akan magudanan ruwa

Ambaliya:Gwamnatin Kano za ta rushe gine-ginen da akayi akan magudanan ruwa

Date:

Mukhtar Yahya Usman

 

Gwamnatin Kano ta kafa kwamiti na musamman da zai bibiyi matsalar ambaliyar ruwa da ake fuskanta a kwanakin nan.

 

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai Malam Muhammadu Garba ya fitar ranar Litinin.

 

Muhammadu Garba ya ce gwamnatin Kano ta damu kwarai da ambaliyar da ake samu wadda ta haddasa matsaloli masu yawa a cikin birnin Kano.

 

Ya ce an dorawa kwamitin alhakin nazartar hanyoyin da ke cikin birni da kuma mugudanan ruwa da kwatoci domin gyarasu a kuma gina wasu idan da dama.

 

Haka kuma kwamitin zai duba gine-ginen da aka yi akan magudanan ruwa da sune ke haddasa ambaliyar.

 

Kwamishinan ya kuma jajantawa al’ummar da sukayi asara mai yawa sakamakon ambaliyar.

 

Ya kuma ce jama’a su kara yiwa gwamnatin hakuri a cewarsa za a dauki matakin da ya dace domin magance matsalar.

 

Latest stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...

Related stories

Makiyaya sunyi watsi da dokar kafa hukumar kiwo ta ƙasa.

Makiyaya a kasar nan sun yi watsi da kudirin...

Za’a iya shafe shekaru kafin kawo ƙarshen ƴan bindiga”- Sarkin Musulmi.

Mai Alfarma Sarkin Muslmi, Sultan Sa’ad Abubakar III, ya...