Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, April 26, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniDa dumi-dumi: Kano Pillars za ta sanar da sabon mai horar da...

Da dumi-dumi: Kano Pillars za ta sanar da sabon mai horar da ita a wata mai kamawa-Malikawa

Date:

Mai rikon shugabancin kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars Dr. Ibrahim Galadima ya ce a wata mai zuwa, kungiyar za ta sanar da wanda zai jagoranci Pillars a sabuwar kakar wasannin shekarar 2022/2023.

 

Dr. Ibrahim Galadima ya ce shirye-shirye tuni sun kammala, domin sanar da sabon mai horar da kungiyar ta Sai Masu Gida domin fara shirin tinkarar kakar badi.

 

Dr. Galadima ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun kungiyar Rulwan Idris Malika Garu ya aikewa Premier Radio da safiyar wannan rana.

 

Har ma ya bukaci magoya bayan kungiyar, dama masu ruwa da tsaki da su ci gaba da hakuri da kuma yiwa kungiyar fatan nasara a sabuwar kakar wasanni mai kamawa.

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...