Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiKamfanonin sadarwa, Glo, MTN, Airtel, 9mobile sun roƙi gwamnatin tarayya data basu...

Kamfanonin sadarwa, Glo, MTN, Airtel, 9mobile sun roƙi gwamnatin tarayya data basu damar ƙara kuɗin kira da na data.

Date:

Manyan kamfanonin sadarwar da ke aiki a kasar nan musamman Glo, MTN, Airtel da 9Mobile sun roƙi gwamnatin tarayya da ta ba su damar sauya ƙara kuɗin kira da na data.

Wannan na zuwa ne a yayin da kamfanonin sadarwar ke kira ga Gwamnatin Tarayya da sakar musu mara da kuma neman ta ba su damar gabatar da wannan buƙatar ta hanyar tattaunawa mai ma’ana da masu ruwa da tsaki.

A cewar kamfanonin sadarwar, tsarin ƙayyade musu farashin kuɗin kira da na data na yanzu bai dace da yanayin tattalin arziki ba, don haka suke neman  Kamfanonin sadarwa guda huɗu sun ce su kaɗai ne ba su yi sauya farashinsu ba wanda kuma hakan barazana ga ɗorewar kamfanonin da kuma yiyuwar rage ƙwarin gwiwar masu zuba jari.

Sun bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar haɗin gwiwa da ƙungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ALTON) da Ƙungiyar kamfanonin sadarwa ta Najeriya (ATCON) suka fitar a  Alhamis din nan.

A cewar sanarwar mai ɗauke da sa hannun shugaban ALTON, Mista Gbenga Adebayo, da shugaban ATCON, Mista Tony Emokpere, ba a yi wa tsarin farashin gyara na gaba ɗaya ba a cikin shekaru 11 da suka gabata.

Sun danganta rashin ƙaruwar farashin ga matsalolin da suka shafi ƙa’idojin ƙayyade musu farashi duk da matsalar tattalin arziki da ake fuskanta

Latest stories

Related stories