Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiWani tsagi a jam'iyyar NNPP sun gurfanar da Rabi'u Musa Kwankwaso da...

Wani tsagi a jam’iyyar NNPP sun gurfanar da Rabi’u Musa Kwankwaso da wasu mutane 13 gaban EFCC.

Date:

Wani tsagi a jamiyyar NNPP sun gurfanar da dantakarar shugaban kasa na jamiyyar a zaben 2023 Dr Rabiu Musa Kwankwaso da wasu mutane 13 gaban hukumar yaki da yiwa tattalin arziki zagon kasa EFCC kan zarginsu da wadaka da wasu kudi naira miliyan dubu biyu da rabi mallakin jamiyyar.

Sakataren tsagin dake korafin Oginni Olaposi sun zargi tsohon gwamnan na Kano da laifin almubazzaranci da kudin jamiyyar da aka samu daga sayar da fom din takarar zaben 2023, kudin rajista da yayan jamiyyar ke biya da kuma tallafin da jamiyyar ke samu.

Jaridar Punch ta rawaito Sakataren nacewa halin da jamiyyar ta fada ya sanya ta kasa biyan matasan da suka yiwa jamiyyar aikin tsaron akwatu a zaben 2023 hakkokinsu.

Ya roki shugaban hukumar EFCC da ya bincike halin da asususn jam,iyyar ke ciki tun daga watan maris din 2022 zuwa yau.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...