Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiGwamnatin Adamawa ta rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu nan take.

Gwamnatin Adamawa ta rufe makarantun gwamnati da masu zaman kansu nan take.

Date:

Gwamnatin jihar Adamawa, ta rufe makarantun gwamnatin jihar da masu zaman kansu nan take.

Gwamnatin ta bayar da umarnin rufe makarantun ne jiya Litinin domin rage yaduwar cutar kyanda a tsakanin yara.

Babbar sakatariyar ma’aikatar ilimi ta Adamawa Aisha Umar, ta sanar da sauya ranar komawa makarantar zuwa 13 ga watan Mayun da muke ciki.

Gwamnati ta bukaci duk kan makarantun jihar suyi biyayya ga umarnin, yayin da yara 42 suka rasa rayukan su a jihar sanadiyar cutar kyandar.

Haka zalika ta ce zata cigaba da yin duk mai yiwuwa don tabbatar da an magance annobar cutar a jihar ta Adamawa baki daya.

Wannan na zuwa ne yayin da hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadin cewa cutar kyanda na ci gaba da zama barazana ga yara a Najeriya.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...