Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiFRSC ta buƙaci haɗa hannu da masu ruwa da tsaki domin rage...

FRSC ta buƙaci haɗa hannu da masu ruwa da tsaki domin rage yawaitar haɗura a ƙasar nan.

Date:

Hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa ta bukaci hada hannu da masu ruwa da tsaki a bangaren zirga-zirgar ababen hawa domin rage yawaitar hadura da ake samu a kasar nan.

Hukumar ta FRSC ta gudanar da taron karawa juna sani da direbobi a jihar Sokoto kan yadda za a rage yin lodin wuce kima na dabbobi da kayayyaki da mutane a motoci don rage hadura.

Kwamandan rundunar a Sokoto Mr Abdullahi Maikano, ya ce sun shirya taron ne don lalubo hanyoyin magance matsalolin da ake samu yayin tuki musamman hadura.

Kwamandan rundunar ta FRSC ya nuna damuwear sa karuwar haduran da ake samu a sanadiyar ganganci da gudin wuce sa’a da direbobi suke yi.

Da yake jawabi sakataren kungiyar direbobi ta (NURTW) a jihar Muhammad Labaran, ya yabawa babban kwamandan hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa FRSC Dauda Ali Biu, bisa fito da tsarin ganawa da direbobi da wayar musu da kai kan dabarun tuki don rage yawaitar hadura.

Ya kuma bukaci direbobi dasu kasance masu bin dokokin tuki a duk yanayin da suka tsinci kansu.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...