Saurari premier Radio
30.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiGwamnatin tarayyaGwamnatin tarayya zata gudanar da binciken jiragen sama, don tabbatar da ingancin su.

Gwamnatin tarayya zata gudanar da binciken jiragen sama, don tabbatar da ingancin su.

Date:

Gwamnatin tarayya ta ce hukumar kula da zirga zirgar jiragen sama ta kasa za ta gudanar da cikakken bincike don tabbatar da ingancin duka jiragen sama da ke zirga-zirga cikin ƙasar.

Ministan sufuri Festus Keyamo ne ya bayyana haka ga gidan talabijin na Channels ranar Alhamis.

Ya ce baya ga dakatar da kamfanin Dana da kuma binciken da ake yi wa kamfanin, za a gudanar da bincike a kan duka kamfanonin jiragen sama a ƙasar domin tabbatar da bai wa fasinjoji kariya.

A ranar Laraba ne, Keyamo ya ba da umarnin dakatar da kamfanin na Dana inda ya ce abubuwan da suka faru da jirgin a baya-bayan nan sun saka damuwa a zukatan jama’a.

An dakatar da kamfanin Dana kwana ɗaya bayan da jirgin kamfanin ya zame daga kan titinsa a filin jirgin saman Legas.

 

Latest stories

Related stories