Saurari premier Radio
24.9 C
Kano
Tuesday, May 7, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiHukumomin Burkina Faso sun dakatar da kafofin labaran BBC da VOA daga watsa labarai

Hukumomin Burkina Faso sun dakatar da kafofin labaran BBC da VOA daga watsa labarai

Date:

Hukumomin Burkina Faso sun dakatar da kafofin labaran BBC da na Muryar Amurka, daga watsa shirye-shiryen na tsawon makwanni biyu, saboda watsa rahoton zargin take hakkin bil adama da ake wa sojojin kasar.

A jiya alhamis ne dai kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch, ta ce sojojin Burkina Faso sun kai harin ramuwar gayya yankin Arewacin kasar, inda suka kashe fararen hula 223 ciki kuwa har da kananan yara 56.

A cikin sanarwar da hukumar kula kafofin yada labaran kasar ta fitar, ta ce ta dauki matakin dakatar da kafafen BBC Afrika da VOA ne, bayan wallafa labarai a kafofin sadarwarsu na zamani, da ya zargi sojojin kasar da take hakkin bil adama.

Hukumar ta ce rahoton kafofin yada labaran, na tattare da rashin adalci ga sojojin Burkina Faso bisa zargin da aka yi musu.

Tun a shekarar 2015 ne Burkina Faso da Mali da ke yammacin Afrika, ke fuskantar kalubalen hare-haren masu ikirarin jihadi.

 

Latest stories

Related stories