Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiAtiku Abubakar ya ƙalubalanci yadda shugaban ƙasa da mataimakin sa suka fice...

Atiku Abubakar ya ƙalubalanci yadda shugaban ƙasa da mataimakin sa suka fice daga ƙasar lokaci guda.

Date:

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya bayyana damuwa kan yadda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima suka fice daga kasar nan ba tare da barin wani jagora ba.

A wani tsokaci da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Atiku yace yana ta samun labaran dake nuna cewa, shugaban da mataimakinsa sun fice daga kasar nan.

Atiku yace abin damuwa ne yadda shugabannin biyu za su fice lokaci guda a kasar da ke fuskantar kalubale da dama.

Tsohon mataimakin shugaban ya ce abinda ke damun sa yanzu shi ne, wanene yake jan akalar kasar nan a wannan lokaci?

Inda ya kara da cewa ko itace ke jagorancin kanta da kanta?
Al’umma dai na ci gaba da tsokaci a kan bacewar shugaba Bola Ahmed Tinubu kwanaki 7 da suka gabata, bayan halartar taron zuba jari a kasar Saudi Arabia.

Ya zuwa wannan lokaci babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa, kan inda Tinubun ya shiga, yayin da a yau kuma aka wayi gari da sanarwar cewa mataimakinsa Kashim Shettima zai tafi Amurka domin halartar wani taro.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...