Saurari premier Radio
40.5 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniCristiano Ronaldo zai raba gari da Manchester United

Cristiano Ronaldo zai raba gari da Manchester United

Date:

Dan wasan gaba na kasar Portugal Cristiano Ronaldo ya sanar da zai bar kungiyarsa ta Manchester United ba tare da bata lokaci ba.

 

Kungiyar ta United ce ta sanar da hakan a wani rubutu data wallafa a shafinta na sada zumunta a wannan Talatar cewa ta cimma matsaya na katse kwantaragin Ronaldo.

 

Wannan dai na zuwa ne bayan da Cristiano Ronaldo yayi wata hira da Dan Jarida Piers Morgan, aka kuma wallafa hirar a tashar TalkTV.

 

Matuka ina son Manchester United, kuma ina kaunar kungiyar, haka kuma ina son magoya bayan ta matuka,’ a cewar dan wasa Ronaldo.

 

Yanzu haka dai Ronaldo yana tare da tawagar Portugal a Qatar domin buga Gasar Cin Kofin Duniya, wanda Ronaldo zai jagoranci kasarsa karawa da Ghana ranar Alhamis.

 

Sai dai kungiyar a sanarwar da ta fitar ta kuma wallafa a shafinta na sada zumunta a Talatar nan ta bayyana yiwa dan wasan Fatan nasara da shi da iyalansa kan abin da zai fuskanta a nan gaba’.

 

Ta kuma bayyana cewa tuni ta mayar da hankali kan yadda za ta marawa Erik ten Hag baya da aiki tare, domin mayar da kungiyar kan ganiyar da take bukata.

 

A hirar da Ronaldo yayi da TalkTV a makon jiya, Ronaldo ya ce ”An yaudare ni a kungiyar”, kuma ana ta kokarin sai na bar United ta kowanne hali’

 

Ya kuma ce babu wani ci gaba a kungiyar tun bayan da Sir Alex ya yi ritaya daga horar da kungiyar a 2013.

 

A ranar Juma’a ne dai Manchester United ta fitar da bayanin cewar tana duba hanyar da za ta mayar da martani ga hirar da aka yi da Ronaldo.

 

A tsawon lokacin da Ronaldo ya shafe a kungiyar a duka shekarun da yayi a filin wasa na Old Trafford, ya zura kwallo 145 a wasanni 346 da ya fafata.

 

Mai shekara 37 ya nuna rashin jindadinsa da zama a kungiyar karkashin jagorancin mai horar da ita a yanzu Erik ten Hag.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...