Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiHukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta dakatar da dan wasan gaba...

Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta dakatar da dan wasan gaba na tawagar Super Eagles, Victor Osimhen.

Date:

Hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta dakatar da dan wasan gaba na tawagar Super Eagles, Victor Osimhen.

Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da ɗaya daga cikin manyan mambobin da ke lura da sha’anin hukumar ya fitar a yammacin jiya Laraba.

NFF ta sha alwashin hukunta ɗan wasan ne har sai ya bayar da haƙuri kan wani faifan bidiyo da ya wallafa na caccakar tsohon kocin Nijeriya Finidi George da ya ajiye aiki a bayan nan.

Sanarwar ta ce Osimhen ya ƙetara iyaka kuma hukumar ba za ta lamunci hakan ba, tana mai fatan wannan hukunci ya zama izina ga sauran yan wasan.

An dai samu taƙaddama tsakanin Osimhen da Finidi George tun bayan da kocin ya ƙi sanya shi a wasannin da tawagar Super Eagles ta yi a baya-bayan nan.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories