Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniA wannan rana ta Lahadi za a fara gasar kofin Duniya a...

A wannan rana ta Lahadi za a fara gasar kofin Duniya a Qatar

Date:

Bayan jiran lokaci na karatowar gasar cin kofin duniya da ake jira, a wannan rana ta Lahadi 20 ga Nuwambar 2022, za’a fara gasar cin kofin duniya a kasar Qatar.

 

Gasar wadda kasashe 32 zasu kece raini da juna a wasanni 64 da aka shirya gudanarwa har zuwa wasan karshe.

 

Qatar wadda itace mai masaukin baki, zata karbi bakauncin kasar Ecuador a wasan farko na rukunin A da zai gudana a yammacin Lahadin nan da karfe 5 Agogon Najeriya.

 

Kuma filin wasa na Al Bayt mai daukar mutane sama da 40,000 zai karbi bakuncin wasan na farko, wanda alkalin wasa Daniele Orsato dan kasar Italiya zai jagoranci wasan.

 

Sai dai kafin fara wasan na farko a wannan rana, tuni kasar ta Qatar ta shirya gudanar da bukukuwa da dama, baya ga nuna yadda al’adun kasar suke.

 

Wasanni 64 dai za’a fafata da kasashe 32 daga nahiyoyin kasashen duniya 5 zasu kece raini da juna.

 

Kuma kasar ta Qatar ta gayyaci sanannen malamin addinin musuluncin nan mai da’awa wato Sheikh Zakir Naik domin ya riƙa gudanar da karatuttuka na kira zuwa ga musulunci.

 

Zakir Naik dai zai kasance a Qatar har zuwa ƙarshen wasan na FIFA na bana, wanda yanzu haka ma tuni ya isa ƙasar.

 

Tuni aka raba jadawalin gasar kamar haka………………………….

 

Rukunin A
Qatar
Ecuador
Senegal
Netherlands

 

Rukunin B
Ingila
Iran
Amurka
Wales

 

Rukunin C
Argentina
Saudiyya
Mexico
Poland

 

Rukunin D
Faransa
Australiya
Denmark
Tunisia

 

Rukunin E
Spain
Costa Rica
Jamus
Japan

 

Rukunin F
Belgium
Canada
Moroko
Croatia

 

Rukunin G
Brazil
Serbia
Switzerland
Kamaru

 

Rukunin H
Portugal
Ghana
Uruguay
Koriya ta Kudu

 

A shekarar 2018 dai kasar Faransa itace ta lashe gasar, bayan do ke kasar Crotia a wasan karshe, gasar da ta gudana a kasar Rasha.

Latest stories

Related stories

Kano Pillars ta dakatar da mai horas da ƴan wasanta nan take.

Hukumar gudanarwar kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...