Saurari premier Radio
38.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniPortugal ta lallasa Najeriya da ci 4-0 a wasan sada zumunci

Portugal ta lallasa Najeriya da ci 4-0 a wasan sada zumunci

Date:

Tawagar Najeriya tayi rashin nasara a hannun kasar Portugal da ci 4-0 a wasan sada zumunci da suka fafata.

 

Wasan dai ya gudana a Alhamis dinnan a filin Jose Alvalade da ke birnin Lisbon na kasar ta Portugal.

 

Dan wasa Bruno Fernandes ne ya fara zura kwallon farko a minti na 8 da fara wasan.

 

Kana ya zura kwallo ta biyu a bugun daga kai sai Mai tsaran gida a minti na 34.

 

Bayan dawowa daga hutun Rabin lokaci Dan wasa Gonçalo Ramos ya kara kwallo ta uku a minti na 81.

 

Sai dai Jim kadan kafin kammala wasan Joe Mario ya kara kwallo ta hudu ma kasar sa Portugal a minti na 83.

 

Daga Najeriya kuwa Dan wasa Bonaventure ya barar da bugun daga kai sai Mai tsaran gida a minti na 80 da wasan.

 

Kasar Portugal wadda na cikin kasashe 32 da zasu halarci kofin duniya na wannan shekara, za tai amfani da wasan ne domin kara shiri.

 

Dan wasa Cristiano Ronaldo, dai bai guda wasan ba sabida ciwon ciki da ya ke fama da shi.

 

Daga bangaren Najeriya ma Dan wasanta Victor Osimhen shima bai buga wasan ba sabida rauni da yaji.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...