Hukumar da ke Kula da tsara dokokin kwallon kafa ta duniya IFAB ta ce, za ta tattaunawa batun fara amfani da shuɗin-kati (Blue Card) a wasannin Kwallon kafa.
Ana sanar hukumar ta IFAB za ta gudanar da babban taron ta na Shekara-shekara a cikin watan Maris mai zuwa a kasar Scotland.
Inda ake saran hukumar za ta Tattaunawa batun fara amfani da Shudin-Kati a yunkurin fara amfani da shi a wasannin League na kasashe.
Da zarar amfara amfani da Shudin-Katin, dan wasa zai kwashe minti 10 a wajen fili yana hutawa idan Alkalin wasa ya ba shi shuɗin katin.
A yanzu dai ana amfani ne da katuna biyu, wato kati mai ruwan ɗorawa (Yellow card) a matsayin katin gargaɗi, da kuma jan kati (Red card) a matsayin katin kora da zarar mutum ya yi keta mai girma.
Dama dai ana amfani da shudin kati a wasannin kwallon kafa a mataki na kasa-kasa, sai dai ana sa ran kawo shi cikin manyan gasannin League domin fara amfani da shi.
To amma babu tabbacin ko yaushe za a fara gwajin shudin katin da kuma gasar da za a fara yin gwajin musamman a wasannin nahiyar turai.
Yanzu haka tuni gasar Firimiya ta Ingila ta kushe batun gwajin katin a wasanninta, yayin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta ce bai kamata a fara batun amfani da katin a manyan gasannin duniya ba a yanzu.
Dama wasu na ganin matakin kasar Ingila na kawar da batun ba abin mamaki bane, domin ko a Lokacin fara amfani da na’urar VAR kasar da fari ta kushe batun kafin daga bisani tayi mi’ara koma baya.