Saurari premier Radio
23.8 C
Kano
Saturday, July 27, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiAFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d'Ivoire don marawa Super Eagles...

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Date:

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa birin Abidjan, Côte d’Ivoire don marawa Super Eagles baya a wasan gasar AFCON da ake yi.

Shettima wanda ya tashi ta filin jirgin sama na Abuja, ya tafi kasar don wakiltar Shugaba Bola Tinubu a yunkurin marawa Super Eagles baya.

Mai magana da yawun Mataimakin shugaban kasar Stanley Nkwocha ya ce Shettima ya bar Najeriya ne a yammacin Larabar nan.

Ya ce zuwan Shettima Côte d’Ivoire na dauke cikin umarnin Shugaba Bola Tinubu, duka domin marawa Najeriya baya.

Kawo Yanzu haka dai kasa da sa’a guda za a fara wasan da Super Eagles za ta kece raini da Afrika ta Kudu a wasan kusa da karshe a gasar AFCON da ke gudana a Ivory Coast.

Wasa tsakanin kasashen biyun dai zai gudana A a filin Wasa na Stade de la Paix da ke birnin Bouake a kasar ta Côte d’Ivoire .

Latest stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

Related stories

246943801721751646

246943801721751646

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...