Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiYadda mutum uku suka mutu saboda kallon wasan Najeriya da Afirka ta...

Yadda mutum uku suka mutu saboda kallon wasan Najeriya da Afirka ta Kudu

Date:

Tsohon dan majalisar tarayya mai wakiltar karamar hukumar Ika a jihar Delta kuma jigo a jamiyyar APC, Cairo Ojougboh ya mutu yayin da yake tsaka da kallon wasan Najeriya da Afrika ta Kudu a yammacin ranar Laraba.

Wata majiya daga iyalan mamacin ta ce ya mutu a yayin da aka soke kwallon da Najeriya ta ci kuma aka soke inda bai wa Afrika ta Kudu bugun daga kai sai mai tsaron raga, da hakan ta sa kasar ta farke kwallon da Najeriya ta zura mata.

Shima wani mataimakin mai kula da sashin kudi na jami’ar Kwara Alh. Ayuba Abdullahi, ya rasa ransa lokacin da yake kallon wasan tsakanin Najeriya da Afirka ta Kudu.

Ya kalli wasan tun daga farko har zuwa bugun fenareti kafin mai afkuwa ta afku.

Baya ga wannan wasu rahotanni sun tabbatar da wani mai hidimar kasa na NYSC a jihar Adamawa, shi ma ya rasu yayin da yake kallon kwallon da Najeriya ta yi da Afirka ta Kudun, a wani gidan kallon da ke garin Numan.

Matashin Samuel dan jihar Kaduna ya rasu ne kafin bugun karshe na fanaretin da Najeriya ta samu nasara.

Shugaban ofishin NYSC na jihar Adamawa, Jingi Dennis ya ce an tabbatar da rasuwar dan mai hidimar kasar, bayan an kai shi babban asibitin garin na Numan.

Wannan ya sa adadin wadanda aka tabbatar sun mutu yayin Kallon wasan Najeriyar da Afirka ta Kudu ya kai mutum 3.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...