Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniNPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi...

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Date:

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars wasa Uku domin tayi nasara ko kuma a dauki mataki mai tsari kan kungiyar.

Mai rikon Kwamishinan Matasa da Wasanni da ke shirin barin gado Hon. Hamza Safiyanu Kachako ya ce Gwamnati ta bawa shugabancin kungiyar da Yan wasan adadin wasanni Ukun domin su samu nasara.

Hamza Kachako a wata sanarwa da ya fitar a Juma’ar nan ya ce waadin ya zo ne sakamakon yadda kungiyar bata kokari musamman a wasannin da take bugawa a gida da waje a kakar wasannin 2023/2024.

Ya Kuma ce abin takaicine irin rashin kokarin da kungiyar ba tayi musamman wasan makon da ya gabata da Pillars din tayi rashin nasara da ci 2-1 a hannun Bendel Insurance a Benin.

Ya kuma bayar da misalin rashin nasara da kungiyar tayi a wasannin da Pillars tayi rashin nasara kamar na Shooting Stars da na Enyimba.

Kachako ya ce Gwamnatin Kano karkashin Gwamna Abba Kabiru Yusuf ba zata lamunci irin wannan rashin kokarin ba…

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories