Saurari premier Radio
37.4 C
Kano
Thursday, May 2, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniDa dumi-dumi: Evans Ogenyi ya zama sabon mai horar da Kano Pillars

Da dumi-dumi: Evans Ogenyi ya zama sabon mai horar da Kano Pillars

Date:

Ƙungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta sanar da Evans Ogenyi a matsayin sabon babban mai horar da tawagar.

 

Evans wanda a baya tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Warri Wolves, zai jagoranci kungiyar a kakar wasannin shekarar 2022/2023.

 

Mai magana da yawun kungiyar Lurwan Idris Malikawa Garu ne ya bayyana hakan a zantawarsa da Ahmad Hamisu Gwale da safiyar wannan rana.

 

Malikawa ya ce Ƙungiyar karkashin shugabancin Dr Ibrahim Galadima ne ya sanar da amincewa da nadin Evans sabon Mai horar da Pillars din.

 

Ibrahim Galadima ya ce cikin masu horarwa 31 da suka Mika bukatar horar da Pillars, sun karbi na mutum 14 ne.

 

Wanda kuma cikinsu biyar daga kasashen waje suke, kamar daya daga kasar Mexico, sai biyu da suka fito daga Ghana, da daya daga Cote d Ivoire haka ma daya daga kasar Togo.

 

Yanzu haka dai Evans Ogenyi ya zama babban horarwa na kungiyar, sai Ibrahim A. Musa da zai tai makamasa.

 

Haka zalika Ahmad Garba Yaro Yaro da Gambo Muhammad zasu kasance mataimakan masu horarwa.

 

Inda kuma Abbas Auwalu zai zama Mai horar da masu tsaran raga na kungiyar.

Latest stories

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...