Saurari premier Radio
26.9 C
Kano
Friday, February 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniJerin kasashe 16 da zasu buga wasa zagaye na 16 a kofin...

Jerin kasashe 16 da zasu buga wasa zagaye na 16 a kofin duniya

Date:

Bayan da gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 ke ci gaba da gudana a kasar Qatar, tuni a wannan rana wasanni zasu ci gaba da gudana.

 

Lamarin da ke nuni da wasanni zagaye na kasashe 16 za a ci gaba da fafawa, bayan kammala wasanni rukuni.

 

Jumulla dai kasashe 32 ne suka fafata gasar, da kuma kasa daya ce Zata zama zakara a wasan karshe da zai gudana a filin wasa na Lusail a ranar 18 ga Disambar da muke ciki.

 

Sai dai abu mafi kayatarwa da Kuma burgewa shi ne, kasashe biyu cikin biyar a nahiyar Afrika da suka halarci wannan gasa, sune kawai suka samu damar kaiwa ga zagaye na kasashe 16.

 

Wato Morocco da ta kammala a mataki na farko a rukunin D da maki 7, sai kuma Senegal wadda ta kammala da maki 6 a rukunin A na wannan gasa…

 

Cikin wasannin da zasu gudana bari mu fara da wasan farko na zagayen kasashe 16 da za ai gumurzu a Asabar dinnan 3 ga Disamba…

 

Netherlands da Amurka a filin wasa na Khalifa International Stadium da karfe 4 na yamma.

 

Sai Argentina da Australia a filin wasa na Ahmad Bin Ali Stadium da karfe 8 na dare.

 

A ranar Lahadi 4 ga Disamba kuwa….

 

France da Poland a filin Al Thumama Stadium da karfe 4 na yamma.

 

Yayin da England da Senegal a filin wasa na Al Bayt Stadium da karfe 8 na dare.

 

A ranar Litinin 4 ga wata kuwa..

 

Japan zata kece raini da Croatia a filin Al Janoub Stadium da karfe 4 na yammaci.

 

Sai kasa Mafi lashe wannan gasa Brazil zata buga da Koriya ta Kudu a filin Stadium 974 da karfe 8 na dare.

 

Haka zalika a ranar Talata 5 ga watan na Disamba kuwa..

 

Morocco da kasar Spain a filin wasa na Education City, wasan da zai gudana da karfe 4 na yammacin ranar.

 

Sai kuma Portugal da Switzerland a filin wasa na Lusail Stadium, da karfe 8 na daren ranar.

 

1_Netherlands
2- Amurka
3-Argentina
4-Australia
5-Japan
6-Croatia
7-Brazil
8- Koriya ta Kudu
9-England
10-Senegal
11-France
12- Poland
13-Morocco
14- Spain
15-Portugal
16-Switzerland

Latest stories

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...