Saurari premier Radio
34.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniAl-Nassr ta yiwa Ronaldo tayin Yuro 200m duk shekara

Al-Nassr ta yiwa Ronaldo tayin Yuro 200m duk shekara

Date:

Kungiyar kwallon kafa ta Al-Nassr ta kasar Saudi Arabia, ta yiwa Dan wasa Cristiano Ronaldo tayin komawa kungiyar.

 

Dan kasar Portugal da a yanzu ba shida kungiya, kuma na tare da tawagarsa da suke fafata gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 a Qatar.

 

Jaridu daga Kasar Sifaniya sun rawaito cewa kungiyar da dan wasan zasu amince da juna ya fara buga wasa a ranar 1 ga Janairu Mai zuwa.

 

Mai shekara 37 ya bar tsowuwar kungiyarsa ta Manchester United kwana biyu kafin fara kofin duniya.

 

Gwarzan kyautar Ballon d’Or har sau biyar, yanzu haka Al-Nassr ta amince da biyanshi Yuro 200m, kwatan kwacin Fan dubu miliyan 172 duk shekara.

 

Dan wasan ya bar Manchester United ne bayan hira da Dan jarida Piers Morgan daga gidan talabijin na Talk TV da a lokacin ya ce kungiyar bata yi masa adalci ba.

 

Cristiano Ronaldo ya zura kwallo 145 a wasa 346 da ya yi wa United a karo biyu da ya buga mata wasa.

 

Lamarin da ke nuna bayan da ya je Real Madrid a 2009, kana ya koma Old Trafford daga Juventus a shekarar 2021.

 

Sai dai a kakar wasannin shekarar 2020 da 2021, Al-Nassr ba ta lashe kowacce gasa ba.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

NPFL: Gwamnatin Kano ta bawa Kano Pillars wasa Uku domin ta yi Nasara

Gwamnatin Jihar Kano ta bawa kungiyar Kwallon kafa ta...