Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniEden Hazard ya sanar da yin murabus daga bugawa Belgium wasa

Eden Hazard ya sanar da yin murabus daga bugawa Belgium wasa

Date:

Kyaftin kasar Belgium Eden Hazard ya sanar da yin murabus daga bugawa kasar sa wasa.

 

Hazard ya bayyana haka ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta Instagram a wannan rana ta Laraba.

 

Dan wasan wanda ke wasa a Real Madrid ta kasar Sifaniya, ana kallon matakin na da alaka da ficewa tin a matakin rukuni da kasar ta Belgium tayi a gasar kofin duniya ta shekarar 2022 da ke gudana a Qatar.

 

Eden Hazard ya buga wasa 126 da cin kwallo 33 a duka fafata da yayiwa kasar sa.

 

“Kwarai Ina godiya gareku matuka, bisa goyan baya da Kuma fatan alkhairi da kuka nuna min, a cewar Hazard a sakon da ya wallafa a shafinsa na Instagram.

 

Ya ce ya dauki matakin ne domin samun hutu da kuma bawa wasu damar da suma zasu nuna bajintarsu.

 

Mai shekara 31 Hazard tin a shekarar 2008 ya fara bugawa Belgium wasa, sai dai har kawo yanzu babu wani kofi da ya lashe a matakin kasar ta Belgium.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...