Saurari premier Radio
39.8 C
Kano
Friday, April 12, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniWasannin da zasu gudana a kofin duniya a wannan Juma ar

Wasannin da zasu gudana a kofin duniya a wannan Juma ar

Date:

Bayan hutun kwanaki biyu a gasar cin kofin duniya da ke gudana a Qatar.

 

A wannan rana ta Juma’a 9 ga Disambar da muke ciki, za a ci gaba da fafata gasar ta shekarar 2022.

 

Zagayen dab dana kusa da karshe a gasar za a ci gaba a yammaci da kuma daren wanann Juma ar.

 

Kasar Crotia wadda tayi rashin nasara a wasan karshe a shekarar 2018 zata kece raini da Brazil da ta fi kowacce kasa lashe wannan gasa.

 

Wasan zai gudana da karfe 4 a filin Education City Stadium, karkashin jagorancin Michael Oliver dan kasar Ingila.

 

Haka zalika itama kasar Netherlands wadda a shekarar 2012 tayi rashin nasara a hannun Sifaniya, zata barje gumi da Argentina da itama a shekarar 2014 taji babu dadi da ci 1-0 a hannun Jamus.

 

Wasa tsakanin kasashen biyun zai gudana da karfe 8 na dare, a katafaren filin wasa na Lusail wanda nan ne za a buga wasan karshe a wannan gasa.

 

Kuma ana saran Dan kasar Sifaniya Antonio Mateu Lahoz shi ne zai jagoranci fafatawar .

 

Abin jira a gani shi ne kowacce kasa ce zata kai wasan kusa da karshe a wannan gasa ta shekarar 2022 da ke gudana a Qatar.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...