Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Wednesday, April 10, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiWasanniQatar 2022 : Dan Jaridar Amurka Grant ya mutu a bakin aiki

Qatar 2022 : Dan Jaridar Amurka Grant ya mutu a bakin aiki

Date:

Fitaccen Mai gabatar da labarin wasannin kasar Amurka Grant Wahl, ya mutu a ranar Juma’a sakamakon yanke jiki da yayi .

 

Lamarin ya faru da Dan Jarida Grant yana tsaka da kawo abin da ke faruwa a wasan dab dana kusa da karshe da ya gudanatsakanin Argentina da Netherlands a gasar cin kofin duniya a Qatar.

 

Mista Wahl wanda ke fama da rashin lafiya kusan kwanaki goma da suka gabata, sai dai kafin mutuwarsa ya bayyana ya na cikin koshin lafiya.

 

Dan Jarida Mista Grant Wahl ya shafe akalla karni biyu yana kawo labaran wasanni, Kuma ya halarci tare da kawo abin da ke wakana a kofin duniya akalla 11, kamar yadda shafinsa ya bayyana.

 

Grant Wahl Mai shekara 48 ya dawo gabatar da labarai, bayan da aka hanashi shiga filayen wasanni a Qatar saboda sanya riga Mai launin bakan gijo.

 

Har kawo yanzu dai ba a fayyace musabbabin mutuwarsa ba, amma ana ta yabo daga hukumar Kwallon Kafa ta Amurka, da Lebron James, da Kwamishinan MLS Don Garber, Peter King, Marc Stein da sauran mutane da dama a shafin Twitter.

Latest stories

Gov. Yusuf Clashes with Ganduje over Governance Failure Accusations

Karibu Abdulhamid Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, and...

Related stories

AFCON 2023: Kashim Shettima ya tafi Cote d’Ivoire don marawa Super Eagles baya

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya bar Najeriya zuwa...