Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Friday, May 17, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiƳan majalisa sun zargi wasu masu ruwa da tsaki a harkan mai...

Ƴan majalisa sun zargi wasu masu ruwa da tsaki a harkan mai dayin zagon kasa ga tattalin arziki.

Date:

Kwamitin kula da harkokin albarkatun man fetur na majalisar wakilai, yayi kiran ga jami’an tsaro da su dirarwa yan kasuwa dake boye man fetur din su da kuma tsawwala farashinsa yadda suka ga dama.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabannin kwamitocin biyu, Ikenga Ugochinyere da Henry Okojie, yan majalisar sun bayyana cewa, sun isar da sakonni ga masu ruwa da tsaki a harkar rarraban albarkatun mai da su kawo karshen dogayen layukan mai a fadin kasar nan.

Yan majalisar sun zargi wasu masu ruwa da tsaki a harkar mai da yin zagon kasa ga tattalin arzikin kasa, inda su ka bukaci cibiyoyin tsaro da su taka musu birki.

Yan majalisar sun ce sun gana da wasu bangarori kamar su kamfanin mai na kasa, da hukumar kula da sa ido wajen rarraba man, da kungiyar dillalan mai ta kasa da kungiyar masu motocin dakon man ta kasa.

Sanarwar ta kara da cewa, daga abinda bincikensu ya gano, tabbas akwai wadataccen man fetur a kasa.

Kwamitocin sun tabbatar da cewa, a yanzu an shawo kan matsalar kuma nan da yan kwanaki, karancin man zai zama tarihi.

Latest stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...

Related stories

Kananan Hukumomi 14 A Kano Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A Bana

Mukhtar Yahya Usman Hukumar kula da yanayı ta kasa NİMET...