Saurari premier Radio
34.4 C
Kano
Saturday, December 2, 2023
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan sanda sun dakile wani harin yan bindiga a Tsafe dake Zamfara.

Yan sanda sun dakile wani harin yan bindiga a Tsafe dake Zamfara.

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

 

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Zamfara, ta yi nasarar hallaka wasu yan bindiga 2 tare da dakile harin da suke shirin kaiwa wani kauye a karamar hukumar Tsafe.

 

Wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Muhammad Shehu, ya fitar a Litinin din nan a Gusau babban birnin jihar, ta ce kwamishinan ‘yan sanda na Zamfara, CP Kolo Yusuf ya yaba da jajircewar ‘yan sandan da suka dakile gari.

 

Ya kuma tabbatar wa mazauna yankin cewa rundunar ta himmatu sosai wajen dakile sake bullar miyagun laifuka a fadin jihar.

 

Kakakin yan sandan jihar Muhammad Shehu ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da baiwa jami’an tsaro goyon baya a kokarinsu na dawo da dawwamammen zaman lafiya da tsaro a jihar.

 

Ya ce rundunar za ta ci gaba da inganta tare da cigaba da yaki da ‘yan bindiga a jihar.

Latest stories

Related stories