Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiYan bindiga sun saki tsohon mataimakin gwamnan jihar Nassarawa

Yan bindiga sun saki tsohon mataimakin gwamnan jihar Nassarawa

Date:

Karibullah Abdulhamid Namadobi

An sako tsohon mataimakin gwamnan jihar Nassarawa Farfesa Onje Gye-Wado da wasu ‘yan bindiga suka sace ranar 7 ga watan Afrilu.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar DSP Ramhan Nansel ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau Litinin.

DSP Ramhan Nansel ya ce tsohon mataimakin gwamnan ya samu iskar yanci ne da misalin karfe 9:00 na daren ranar Lahadi data gabata, kuma ya sake haduwa da iyalansa.

Ya kara da cewa ‘yan sandan ba su da masaniyar wani kudin fansa da aka biya kafin a sako shi.

A cewarsa, an saki shine ne saboda matsin lamba da hadin gwiwar jami’an tsaro suka yi wa masu garkuwa da mutanen.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...