Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiKiwon LafiyaYan Najeriya miliyan 60 suna fama da matsalar kwakwalwa

Yan Najeriya miliyan 60 suna fama da matsalar kwakwalwa

Date:

A yau ne ake bikin ranar lafiyar kwakwalwa ta duniya, majalisar dinkin duniya ta ware duk ranar 10 ga watan oktober domin tunasar da alummar duniya amfanin kula da lafiyar kwakwalwar su, An fara bikin ranar ne a shekarar 2014.

Taken bikin na bana shine lafiyayiyar kwakwalwa hakki ne ga kowanne biladama a fadin duniya.

Bincike ya nuna cewa Najeriya na da kusan cibiyoyi da asibitocin lura da masu tabin hankali sama da 200, wadanda suka yi karanci matuka wajen lura da mutanen kasar nan sama da miliyan 200, wadanda ciki akwai masu cutar da ke da alaka da tabin hankali da aka kiyasta za su kai miliyan 50 zuwa miliyan 60.

Bisa wannan kiyasin, ya zama likitan kwakwalwa daya ne zai lura da mutum miliyan daya, ga kuma rashin asibitoci ko cibiyoyin lura da marasa lafiyar kwakwala.

Jihohin da kuma suke da cibiyoyin, yawancin sun lalace kuma ba a lura da su yadda ya kamata. Sai kuma wasu jihohin da suke da asibitocin tarayya da ke kula da masu tabin hankalin.

Hakan yasa masana ne suke ganin asibitocin sunyi kadan su kula da adadin masu matsalar kwakwalwar.

 

 

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...