Saurari premier Radio
37.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiBabu maganar dawo da biyan tallafin man fetur gaba daya a Nijeriya...

Babu maganar dawo da biyan tallafin man fetur gaba daya a Nijeriya cewar babban jami’in gudanarwa na kamfanin kula da albarkatun mai na kasa (NNPCL)

Date:

Babban jami’in gudanarwa na kamfanin kula da albarkatun mai na kasa (NNPCL), Mele Kyari, ya jaddada cewa, babu maganar dawo biyan tallafin mai gaba daya a Nijeriya.

Ya shaida hakan ne a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan wata ganawa da ya yi da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Idan za a tuna dai, shugaban kungiyar (PENGASSAN), Festus Osifo, a ranar Jama’a ya yi ikirarin cewa, gwamnati ta dawo da biyan tallafin mai, duk da cewa, gwamnatin ta janye tallafin man ferur din tun a watan Mayu.
A nasa jawabin, Shugaban kamfanin NNPCL Kyari, ya yi bayanin cewa, sayar da mai da ake yi a wasu jihohi akan farashi mai sauki ba shi ke nufin an dawo da biyan tallafin man fetur ba.
Dangane da dogon layukan mai da ake samu a wasu gidajen mai a sassan kasar nan, Kyari ya ce, matsalar ta samu asali ne sakamakon rufewar wasu hanyoyin da man ke bi zuwa matattararsa na arewacin kasar da ya ke taso wa daga kudancin kasar nan, hakan ya janyo tsaikon samar da isashshen man a wasu wurare.

Latest stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...

Related stories

Sarkin musulmi ya ja hankalin shugabanni kan samarwa da al’umma makoma

Mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar na 3...