Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane da dama tare da kashe wasu...

‘Yan bindiga sunyi garkuwa da mutane da dama tare da kashe wasu a garin Yola dake karamar hukumar Karaye dake nan jihar Kano.

Date:

Ana zargin ‘yan bindiga sunyi garkuwa da mutane da dama tare da kashe wasu a kauyen Yola dake karamar hukumar Karaye a nan jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga kauyen na Yola dake karamar hukumar ta Karaye a ranaku daban daban na makonnin da suka gabata tare da sace mazauna kauyen goma sha daya.

Majalisar Dokokin Kano Ta Amince Da Kudirin Gyaran Dokar Masarautun Jihar.
Haka zalika wasu da suka zanta da Premier Radio kuma suka nemi a sakaye sunan su saboda fargabar abinda kaje yazo, sunce ‘yan bindigar sun kashe mutane da dama yayin farmakin nasu.

Mutanen sun kuma bukaci rundunar ‘yan sanda da gwamnatin jihar Kano data kai musu daukin gaggawa ta hanyar samar da sansanin jami’an tsaro a yankin domin dakile satar mutane da ‘yan bindigar keyi a yankin na karamar hukumar Karaye.

Duk kokarin da mukayi don jin tabakin rundunar ‘yan sandan Kano kan wannan al’amari lamarin ya ci tura.

Mai magana da yawun rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce zai bincika saidai har kawo lokacin hada wannan rahoto bai tuntube mu ba.

Wannan dai bashi ne karon farko da akan samu rahotannin yin garkuwa da mutane a wasu daga cikin kauyuka dake kananan hukumomin Kano lamarin dake bukatar daukin gaggawa daga mahukunta.

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...