Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Saturday, May 18, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiMajalisar wakilan kasar nan zata fara raba motocin alfarma ga mambobin majalisar

Majalisar wakilan kasar nan zata fara raba motocin alfarma ga mambobin majalisar

Date:

Majalisar wakilan kasar nan zata fara raba motocin alfarma ga mambobin majalisar a makonni masu zuwa.

Mai magana da yawun majalisar Akin Rotimi, ya ce za a rabawa ‘yan majalisar motocinne domin gudanar da ayyukan ofis bana kashin kai ba.

Ya ce irin wadannan motoci ana baiwa ‘yan majalisa kuma suna mayar dasu da zarar sun kammala wa’adin su.

Dokar kafa hukumar kula da kayayyakin morewa rayuwa da gwamnati ke samarwa ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano.

Saidai wani abun tambaya anan shine ina irin wadannan motoci da aka baiwa ‘yan majalisar da suka gabata, kuma idan har ‘yan majalisar na dawo da irin wadannan motoci mai yasa ba za a baiwa na yanzu ba har sai an siyo sabbi.

Akin Rotimi, ya kara da cewa motocin ba kawai ana sayen su ga ‘yan majalisa bane kawai suma wadanda gwamnati ta nada a mukamai daban daban ana saya musu irin wadannan motoci.

Idan za a iya tunawa dai kafafen yada labarai sun ruwaito cewa kowane dan majalisa zai samu moto kirar SUV mai darajar naira miliyan 200 saidai mai magana da yawun majalisar ya ce ana kambama zancenne kawai.

Latest stories

Related stories