Saurari premier Radio
33.9 C
Kano
Saturday, May 4, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiTinubu ya soki yinkurin Atiku na shigar da sabbin shaidu gaban kotun...

Tinubu ya soki yinkurin Atiku na shigar da sabbin shaidu gaban kotun koli

Date:

Kabiru Bello Tukur

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu yace abinda Jamiyyar PDP da ɗan takarararta Atiku Abubakar ke kokarin yi na shigar da sabbin shaidu a gaban kotun koli cikin shari’ar kujerar zaben shugaban kasa na 2023 ba mai yiwuwa ba ne.

Jamiyyar PDP da da takarar ta Atiku Abubakar na kalubalantar hukuncin kotun daukaka kara da ta tabbatar da nasarar Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023, inda suka yi zargi Tinubu da ha’inci wajen gabatar da takardun karatu na bogi dake cike da almundahana.

A yanzu Atiku Abubakar na kokarin samun sahalewar kotun domin gabatar mata da wadannan sabbin shaidu.

Jami’ar Amurka ta fitar da takardun karatun Tinubu

Sai dai a martanin da ya gabatarwa da kotun shugaba Bola Tinubu ta hannun lauyoyin sa karkashin jagorancin Wole Olanipekun SAN, shugaban yace Kotun bazata yi la’akari da takardun Karatun sa da Atiku ya samo daga Jami’ar Chicago ba.

Tinubu yace kotun bata da ikon amsar shaida a rubuce daga Magatakardar Jami’ar Chicago saboda kasancewar baya cikin shaidu da suka bayyana a gaban kotun sauraran karar shugaban ƙasar tun farko kamar yadda sashi na 41, ɗaya cikin baka na kundin dokar zabe na 2022 ya tanada
cewa kotu ba zata iya amfani da rubutacciyar shaidar da mai ita bai bayyana gaban kotun ya amsa tambayoyi ba.

Kuma a bayyane take cewa shi wannan shaida da Atiku ke son gabatarwa bai gabata gaban kotun sauraran kararrakin zaben ba sam.

A karshe Tinubun yayi kukan cewar in har kotun koli ta karbi sabbin shaidu da ake son gabatar mata to kuwa ba zai samu damar mayar da martani yadda yakamata ba, wanda kuma yin haka rashin adalci ne

Ya kara da cewa karbar sabbin shaidu zai sake bude kofar sabuwar tattaunawa a shari’ar wadda kuma kotun bata da hurumin yin hakan kasancewar kwanaki 180 na yin haka da tsarin mulki ya tanadar sun riga sun shuɗe, a don haka ya roƙi kotun ƙolin da tayi watsi da bukatar iznin gabatar da sabbin shaidun da Jamiyyar PDP da ɗan takarar ta Atiku Abubakar suka miƙa gabanta.

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...