Saurari premier Radio
35.9 C
Kano
Sunday, May 5, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabarai'Yan Jarida na aiki cikin mawuyacin yanayi a kasar nan cewar ministan...

‘Yan Jarida na aiki cikin mawuyacin yanayi a kasar nan cewar ministan yada labarai.

Date:

‘Yan Jarida na aiki cikin mawuyacin yanayi cewar ministan yada labarai.

Gwamnatin tarayya ta ce ‘yan jaridar kasar nan na aiki cikin yanayi mai wahala tana mai cewa ‘yan jarida na bukatar yanayin gudanar da aiki mai kyau.

Ministan yada labarai da wayar dakai na kasa Muhammad Idris ne ya bayyana haka a tattaunawar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN.

Idris, wanda ya ce wasu ’yan jarida suna sadaukar da kansu a yayin gudanar da ayyukansu, ya kuma ba da tabbacin cewa zai yi aiki a cikin abubuwan da gwamnati ke da su don inganta ayyukansu.

“Alawus da ake baiwa ‘yan jarida batu ne dake cigaba da fuskantar kalubale kuma mun yarda cewa ‘yan jarida na bukatar a karfafa musu gwiwa tare da samun kudaden su.

“Saboda suna aiki cikin mawuyacin yanayi kuma suna sadaukar da rayuwar su kamar jami’an soji.

“Wasu lokutan ana hada ‘yan jarida da sojoji wajen yaki da ‘yan ta’adda inda sukan dawo da raunuka kaga abinda ya faru a Zamfara yadda Dan jarida ya rasa ransa saboda ayyukan ‘yan bindiga,” a cewar ministan.

Ministan yada labaran ya kuma ce mai yasa gwamnati ba zata iya sanya ‘yan jarida cikin tsarin karin albashi ba, yana mai cewa akwai bukatar a kalli matsalolin da aikin yake fuskanta tare da magance su.

” Ina goyon bayan ‘yan jarida suyi rayuwa mai kyau ,” a cewar minista Muhammad Idris.

Aminu Abdullahi Ibrahim

Latest stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...

Related stories

2023 ita ce shekara mafi muni ga yan jarida.

Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan'adam ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta...