Saurari premier Radio
23.5 C
Kano
Tuesday, July 23, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiJami'ar tarayya dake Gusau ta gargadi dalibai dake gidajen kwanan dalibai na...

Jami’ar tarayya dake Gusau ta gargadi dalibai dake gidajen kwanan dalibai na wajen makaranta

Date:

Jami’ar tarayya dake Gusau a jihar Zamfara ta gargadi dalibai da suke kwana a gidajen dake wajen makaranta a yankin Damba dasu canza matsugunni zuwa wani guri na daban don kaucewa ‘yan bindiga.

Cikin sanarwar da jami’in yada labaran jami’ar Umar Usman ya fitar, ta shawarci daliban dasu koma cikin garin Gusau ko yankin Sabon Gida dake samun kulawar jami’an tsaro.

Gargadin ya biyo bayan sace wasu dalibai hudu da akayi a gidajen kwanan dalibai dake Damba.

Tuni dai dakarun sojin kasar nan na Hadarin Daji suka kubutar da daliban hudu.

Usman ya ce daliban dake zaune a wajen Gusau musamman Damba sune suka fi fuskanar barazanar ‘yan bindiga.

Masu garkuwa da mutane sun sace dalibai 25 tare da masu aikin gini tara a wajen Gusau a ranar 21 ga watan Satumba sai dai an kubutar da wasu daga cikin su yayin da har yanzu mutane 12 ke cigaba da kasancewa a hannun ‘yan bindigar.

 

Aminu Abdullahi Ibrahim

Latest stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...

Related stories

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA AMURKA.

SANARWAR JANYEWA DAGA TAKARA DAGA SHUGABA JOE BIDEN NA...

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP.

An samu rabuwar kai a Jamiyyar PDP na bayyana cewa, An...