Saurari premier Radio
31.9 C
Kano
Sunday, May 19, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiEU tayi Allah wadai da mahukantan Chadi game da zaɓen da ya...

EU tayi Allah wadai da mahukantan Chadi game da zaɓen da ya gudana a ƙasar.

Date:

Kungiyar Tarayyar Turai, ta yi tir da All…wadai da yadda mahukuntan kasar Chadi suka hana masu sanya idanu kan zaben kasar kusan dubu 3 gudanar da aikin su yadda ya dace.

Mafi yawan masu sanya idanun da aka hana gudanar da aiki yadda ya dace na cikin tawagar da EU din ta dauki nauyi.

Tuni dai yan adawa suka bukaci a kauracewa zaben a cewar su an tafka manyan kura kurai da kuma tafka magudi.

Suma dai kungiyoyin da suka shiga kasar don sanya idanu game da zaben sun ayyana shi a matsayin wanda ke cike da kura-kurai ganin yadda gwamnati ta gaza yin komai da ya shafi zaben a bayyane.

Har yanzu dai ana dakon sakamakon zabe, wanda bashi da wani armashi kasancewar ‘yan adawa basu yi wani karsashi a zaben ba.

To sai dai hakan bai zo da mamaki ba, kasancewar dama an yi hasashen hakan tun kafin zuwa zabe, la’akari da yadda gwamnatin rikon kwarya ta rika murkushe ‘yan adawa ta hanyar hana su tsayawa takara da sauran su.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...