Saurari premier Radio
29.9 C
Kano
Saturday, June 15, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiMamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Mamakon ruwa a Filato ya lalata gidaje, makarantu da asibitoci.

Date:

Wani mamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya ya lalata gidaje 200 da ajujuwan makarantu da asibitoci a Miango, dake Karamar Hukumar Bassa da ke Jihar Filato.

Sakataren yaɗa labarai na Ƙungiyar ci gaban Matasan Miango, Nuhu Bitrus Nga, ya ce mutane uku kuma sun jikkata a lokacin ruwan kuma suna karɓar magani a asibiti.

Barnar da ruwan saman ya haifar ya ƙara jefa al’ummar Miango da suka sha fama da munanan hare-hare da kuma gudun hijira a cikin wani mawuyacin hali a cewar Sakataren yaɗa labarai na Ƙungiyar ci gaban Matasan Miango, Nuhu Bitrus Nga.

Al’ummar yankin sun yi kira ga Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar (SEMA) da Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) da sauransu.

Latest stories

Related stories