Saurari premier Radio
28.9 C
Kano
Monday, May 20, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDa Dumi-dumiShugaban ƙasa Tinubu ya dawo gida Nageriya a yau Laraba.

Shugaban ƙasa Tinubu ya dawo gida Nageriya a yau Laraba.

Date:

Shugaban kasa Bola Tinubu ya dawo gida Najeriya daga ziyarar da kai Turai a yau Laraba.

Shugaban ya samu tarba daga mamnyan mukarraban gwamnati a fadar Villa kamar yadda gidan Talabijin na kasa NTA ya bayyana.

Dama a jiya Talata, mai taimakawa shugabnan kasar kan yada labarai Bayo Onanuga ya sanar a shafin sa nma X cewar shugaba Tinubu zai dawo gida a yau Laraba.

A ranar 22 ga Afrilu ne, Tinubu ya bar Abuja, babban birnin kasar, zuwa Masarautar Netherlands a wata ziyarar aiki.

Wata sanrwa ma daga Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban kasar ya ce shugaban ya ziyarci kasar Netherland ne bisa gayyatar da firaminista Mark Rutte ya yi masa.

Bayan Netherlands, Tinubu ya wuce zuwa birnin Riyadh na kasar Saudiyya domin halartar wani taro na musamman na dandalin tattalin arzikin duniya tsakanin 28 da 29 ga Afrilu.

Latest stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...

Related stories

Atiku yace lokaci ya yi da za a yanke shawarar ko zai kara tsayawa takarar shugaban kasa

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, yace magoya bayan...