Saurari premier Radio
40.9 C
Kano
Monday, May 6, 2024
Saurari Premier Radio
HomeLabaraiDokar kafa hukumar kula da kayayyakin morewa rayuwa da gwamnati ke samarwa...

Dokar kafa hukumar kula da kayayyakin morewa rayuwa da gwamnati ke samarwa ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano.

Date:

Dokar kafa hukumar kula da kayayyakin morewa rayuwa da gwamnati ke samarwa ta tsallake karatu na biyu a majalisar dokokin Kano.

Kudurin samar da dokar kafa hukumar kula da kayayyakin more rayuwa da gwamnati ke samarwa wato (Kano State infrastructure management Agency Bill 2023) ya tsallake karatu na biyu a zauren majalisar dokokin Kano.

Da yake karin haske kan wannan kudirin doka dan majalisa mai wakiltar Ungoggo Aminu Sa’adu ya ce dokar zata tsaftace yadda kamfanonin sadarwa da Satelite da Sola zasu rinka bin dokokin saka su tare da tabbatar da cewa basu cutar da dan adam da dabbobi da muhalli ba.

Ya ce ba a iya jihar Kano za a fara wannan tsari ba domin kuwa tuni wasu jihohin kasar nan suka yi nisa wajen samar da wannan hukuma.

Ya kara da cewa wasu lokutan irin wadannan kamfanoni kan fasa tituna domin sanya wayoyi wanda hakan lalata kayayyakin gwamnati.

Ya ce wannan hukuma zata tabbatar da cewa kamfanonin sun gyara abubuwan gwamnati da suka fasa ko lalatawa yayin gudanar da aikin su.

Ya kara da cewa samar da hukumar ta kula da kayayyakin more rayuwa da gwamnati ke samarwa zai taimaka wajen sanin adadin kwamfanonin da ake dasu a jihar Kano da guraren da suke gudanar da ayyukan su.

‘Kamar wayar nan ta zamani da muke da ita yawanci zaka ga kowane kauye ana da irin wadannan abubuwa.

‘Wadanan abubuwa da muka bijiro dasu shine don mu tsaftace mu tabbatar anayin su bisa ka’ida tare da tabbatar da ingancin kayan domin ana kawo kayan da suke Sub-standard,” a cewar sa.

Gwamnatin Kano ta mika kwarya-kwaryan kasafin kudi na naira biliyan 58 ga Majalisar dokoki

Aminu Sa’adu ya kara da cewa gwamnati zata tabbatar da cewa hukumar ce ke bada izini da karbar harajin da yakamata a karba a wajen kamfanonin.

Latest stories

Related stories